Gwamnatin Kano Za Ta Yi Duk Mai Yi Wuwa Don Samar Da A Asibiti A Unguwar Dangwauro: Abubakar Labaran

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta bada tabbacin yin duk mai yiwuwa wajen samar da wani Katafaren Asibiti Mai Suna Hajiya Khadijah Ibrahim Khalil Pediatric Hospital domin inganta harkar kiwon lafiya a yankin dangwauro dake Karamar hukumar kumbotso.

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Hon. Abubakar Labaran Yusuf shine ya bayyana hakan yayin karbar takardar shaidar mallakar wani Katafaren waje da Kungiyar Cigaban garin dan gwauro wato Dangwauro Development and empowerment Association ta samar da kuma Shaidar Karramawa da suka bashi a ofishin sa.

“Al’ummar Garin Dangwauro karkashin wannan ƙungiya ta Dangwauro Development Community and Empowerment Association gwamnatin Kano ta karbi wannan koke naku kuma zatayi duk mai yiwuwa wajen ganin an samar da wannan Asibiti “.

Ana Bangaren Jagoran kungiyar Malam Ali Bala, Ya bayyana godiya ga gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan cigaba da take kawo jihar Kano sannan yayi kira ga sauran yankuna dasu yi hobbasa suma don gwamnati taji dadin karasa musu.

“Kamar yadda muka sani wannan gwamnati kullum burinta kawo ayyukan cigaba ga Al’umma,wannan ziyara da muka kaiwa Kwamishinan Lafiya yadda ya karbemu ya nuna cewa tabbas Za’a sami wannan Asibiti na Khadijah Ibrahim Khalil Pediatric Hospital a yankin dangwauro, saboda harkar lafiya tana da muhimmanci sosai”.

“Ina kira ga sauran Al’umma dasu yi hobbasa wajen samar da wani aiki na cigaba domin gwamnati ta kawo dauki don amfanin al’umma baki daya “.

“Abin da ya bamu kwarin gwiwa kuma muka karrama Kwamishina shine jajircewarsa saboda yadda ya rike Wannan ma’aikata a baya kuma yayi Abin kirki shine yasa muka Karrama shi”.

Al’umma yankin dai karkashin jagorancin wannan ta cigaban garin dangwauro da kudiri aniyar samar da kyakkyawan yanayi domin amfanin al’ummar yanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *