Gwamnatin Kano Zata Dafawa Aiyukan Hukumar Hisbah Don Yaki Da Badala A Tsakanin Al’umma.

Spread the love

Gwamnatin jahar Kano, ta sha alwashin dafawa aiyukan hukumar hisbah ta jahar kano wajen yaki da badala da tabbatar da kyawawan dabi’u a tsakanin al’ummar jahar Kano.

Mataimakin gwamnan jahar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya bayyana hakan ya yin gudanar da wani taro, na kwanaki uku da hukumar Hisbah ta shirya karkashin jagorancin mukaddashiyar babbar kwamandan hisbah bangaren mata DR. Khadija Sagir Sualiman.

Taron dai an yi masa lakabi da taken ” Hisbah Tayani Mu Gyara”.

Mataimakin gwaman ya godewa DR. Khadija Sagir, bisa wannan yunkuri da ta yi na fito da hanyar nusar da iyaye musamman mata kan kula da tarbiyar yayan su.

Ya ce wajibi ne a farka kuma a tashi tsaya wajen fuskantar matsalolin rayuwar da shafi tarbiyar yaya domin samun al’umma nagari.

A gaggauta bude shagunan da ba a siyar da magani dake mai Karami Plaza Kano: Kotu

Yan sanda sun kama mai sace jama’a da ake nema ruwa a jallo a Abuja

Da ta ke jawabin ya yin gabatar da taron mukaddashiyar babbar kwamandar hukumar hisbah ta jahar Kano, DR. Khadija Sagir Sulaiman, ta bayyana makasudin shirya taron bitar da cewar, lokaci ne da yakamata a yi wa iyaye mata karin tunasarwa kan kula da tarbiyar yayan su, musamman mata , shi yasa suka kira wo ma su ruwa da tsakai kan abinda ya shafi sanin halayyar dan Adam don karin fadakarwa.

DR. Khadija ta kara da cewa sun gaiyoto dalibai mata daga makarantun sakandire na birnin Kano, domin nuna mu su muhimmancin yi wa iyaye biyayya da kuma samun miji nagari.

Taron dai ya samu halattar ma su ruwa da tsaki da al’ummar jahar da ma Makotansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *