Gwamnan jahar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi alkwarin ci gaba da tallafawa manoma da iri, taki, da kuma maganin kashe kwari ga manoman jahar.
Gwamna AbdulRahman, ya bayyana hakan ne a lokacin , da ya kaddamar da fara rabon iri da maganin kashe kwari, ga manoma 10,000 a kananan hukumomi 16 na jahar.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafawa manoman gwiwa , ta hanayar tallafa mu su, da kayan noma.
- Manoma A ĆŠanja Sun Nemi Gwamnatin Jihar Ta Biya Su Diyyar Gonakinsu
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya kama aiki a mukamin da Tinubu ya bashi