Gwamnatin Najeriya ba za ta iya biyan albashin da ‘yan kwadago ke nema ba

Spread the love

Ministan yaɗa labaran Najeriya ya ce gwamnatin tarayya ba za ta iya biyan naira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba, kamar yadda ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta buƙata.

Mohammed Idris ya ce biyan buƙatar ƴan ƙwadagon na nufin gwamnati za ta kashe naira tiriliyan tara da rabi wajen biyan albashin ma’aikata, lamarin da ya ce zai jefa walwalar ƴan Najeriya fiye da miliyan 200 cikin barazana.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja babban birnin Najeriya, ministan ya ce gwamnatin tarayya ta amince da biyan naira dubu 60 a matsayin mafi ƙarancin albashi, wanda ke nufin ƙarin kashi 100 ke nan na ƙarancin albashin, kuma tuni kamfanoni masu zaman kansu suka amince da hakan. Ya ce: “Gwamnatin tarayya ta yi ƙarin kashi 100 na mafi ƙarancin albashin ma’aikata na 2019, amma ƙungiyar ƙwadago na buƙatar a biya naira 494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

“Akwai buƙatar ƴan Najeriya su fahimci cewa gwamnatin tarayya tana da niyyar biyan wadataccen albashi ga ma’aikata, amma a gefe guda, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na ƙoƙarin kauce wa yanayin da zai sa mutane da dama su rasa ayyukansu, musamman daga kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda ba lallai su iya biyan mafi ƙarancin albashin da ƴan ƙwadagon ke bukata ba.

” Ministan yaɗa labaran ya buƙaci ƴan ƙwadagon su koma teburin tattaunawa da gwamnati domin samar da mafita a kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *