Gwamnatin Najeriya na yunƙurin sasanta Dangote da hukumomin man fetur

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin sasanta rikicin saɓanin da aka samu tsakanin matatar mai ta Dangote da kuma hukumomin da ke kula da harkokin man a ƙasar.

Ƙaramin Ministan Man Fetur Heineken Lokpobiri ya ce ya jagoranci wani zama da Aliko Dangote shugaban kamfanin Dangote, da Mele Kyari shugaban kamfanin NNPCL, da Farouk Ahmed shugaban hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), da Gbenga Komolafe shugaban Nigerian Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC) a yammacin yau Litinin.

“Ganawar wani yunƙuri ne na gano maganin matsalolin da matatar ke fuskanta,” in ji ministan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

“Dukkan ɓangarorin sun nuna aniyarsu ta nemo bakin zaren kuma sun nuna jin daɗinsu da yunƙurin sasantawar da ake yi.”

Wannan ne karon farko da ɓangaren gwamnati ya yi magana kan cecekucen da ɓangarorin ke yi bayan hukumomin sun zargi matatar Dangote da fitar da man dizel maras inganci, wanda ta musanta ta hanyar gudanar da gwaji a gaba ‘yanmajalisar tarayya ranar Asabar.

Aliko ya koka kan yadda kamfanonin cikin gida suke ƙin sayar wa matatar tasa ɗanyen man fetur ɗin domin fara tace shi da kuma sayar da shi a Najeriya.

Rahotonni sun ce matatar ta mayar da hankali wajen sayo ɗanyen man daga ƙasashen Libya da Angola domin tace man da za ta fara fitarwa kasuwa a watan Agusta mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *