Gwamnatin Najeriya ta ƙara wa masu yi wa ƙasa hidima alawus zuwa N77,000

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta amince ta ƙara alawus ɗin masu yi wa ƙasa hidima daga naira 33,000 zuwa naira 77,000, wanda zai fara aiki daga Yulin 2024.

An yi ƙarin alawus ɗin ne saboda ƙarin mafi ƙarancin albashi da gwamnatin Najeriya ta yi, kamar yadda kakafin Hukumar NYSC, Caroline Embu ta bayyana a wata sanarwa.

Ta ce sun samu takarda daga Hukumar Albashi ta ƙasa wato National Salaries, Incomes and Wages Commission, wadda shugabanta Ekpo Nta ya saka wa hannu a ranar 25 ga Satumba domin aiwatar da ƙarin alawus ɗin.

A watan Yuli ne Majalisar Dokokin Najeriya suka amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa naira 70,000, wanda shugaban ƙasa ya rattaba hannu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *