Najeriya ta ce za ta kafa wata runduna ta musamman domin kare layuka da cibiyoyin samar da wutar lantarkin ƙasar daga ɓat-gari masu sace kayyakin wutar.
Ministan cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka ranar Juma’a a wata hira da gidan talbijin na Channels da ke ƙasar.
Mista Tunji-Ojo ya ce sun ɗauki mataki tare da takwaransa na wutar lantarki, domin saman da abin da ya kira ”dakarun tsaron lantarki” na ƙasa.
Ya ƙara da cewa za a samar da dakarun ne daga rundunar tsaron fararen hula ta Civil Defence, kuma za a ɗora musu alhakin dakatar da lalata abubuwan lantarkin, lamarin da ke haifar da katsewar wutar a wasu lokuta a faɗin ƙasar.
A baya-bayan nan dai ƙasar na yawan fama da katsewar lantarkin, sakamakon abin da hukumomin ƙasar suka ce sace wasu wayoyin da ɓata-gari suke yi ne ke haifarwa.
Ministan cikin gidan ya ce lokaci yayi da ya kamata a ɗauki matakin bai ɗaya domin magance matsalar.