Gwamnatin Najeriya ta dakatar da wasu manyan jami’an kula da gidajen yarin ƙasar kan zargin karɓar rashawa daga hannun Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.
Wani mai amfani da shafin sada zumunta mai suna Martins Otse da aka fi sani da VerDarMan, cikin wani zargi da ya yi a wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya yi zargin cewa wasu jami’an hukumar EFCC, mai yaƙi da rashawa a ƙasar ta karɓi naira miliyan 15 daga hannun Bobrisky domin jingine shari’ar da ake yi masa da ta shafi liƙin kuɗi a wajen biki, inda kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin wata shida.
Mai amfani da shafin ya kuma yi zargin cewa Bobrisky ya biya wasu miliyoyin kuɗi ga wasu jami’an kula da gidajen yarin, domin ya zaɓi wurin da zai zaune a lokacin da yake zaman gidan yarin.
Tuni dai Bobrisky ya musanta zarge-zargen, yayin da hukumar EFCC da hukumar kula da gidajen yarin ƙasar suka ƙaddamar da bincike kan zarge-zargen.
To sai dai cikin wata sanarwa da hukumar gudanarwar kula da hukumomin gidajen yari da ya kashe gobara ta Najeriya, ta fitar ranar Alhamsi, ta sanar da dakatar da wasu manyan jami’an gidan yarin bisa zargin.
Sanarwar wadda sakataren hukumar Ja’afaru Ahmed ya sanya wa hannu ta ce an dakatar da jami’an ne domin bayar da damar faɗaɗa bincike kan zarge-zargen da aka yi musu, tare da alƙawarta bayyana wa duniya sakamakon binciken.
Jami’an da aka dakatar sun haɗa da Michael Anugwa, Mataimakin Kontirola na hukumar mai kula da gidan yarin Ƙiri-ƙiri mai matsakaicin tsaro da ke Legas, da kuma Sikiru Adekunle, mataimakin Kontirolon hukumar mai kula da gidan yarin ƙiri-ƙiri mai tsananin tsaro.