Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ‘yan kasuwar da ke da ɗabi’ar ɓoye kayan abinci a daidai lokacin da talakawan ƙasar ke cikin matsin rayuwa.
Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin matsin rayuwa da tsadar abinci da ‘yan ƙasar ke ciki.
Ministan ya ce gwamnati a nata ɓangare za ta fito da metri ton 42,000 na abinci daga rumbunan ma’aikatar harkokin noma.
Idongari.ng facebook link https://www.facebook.com/profile.php?id=100089819831293
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.
”Ma’aikatar harkokin noma na da masara da gero da nau’in gari a rumbunan ajiyarta da ke sassan ƙasar daban-daban domin raba wa ‘yan ƙasar nan ba da jimawa ba”, in ji ministan.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ji labarin cewa masu kamfanonin sarrafa shinkafa faɗin ƙasar na da tarin shinkafar da suka taskance, don haka gwamnati ta yi magan da su sun kuma amnce za su fito da metric ton 60,000, don a sayar wa ‘yan ƙasar.
Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ƴan kasuwar da ke ɓoye kayan abinci
Ministan ya ce idan ta kama ma ƙasar za ta ya shigo da abinci daga ƙasashen wajen do magance matsalar tsadar abincin a faɗin ƙasar.
”Nan gaba kaɗan za a yi haka idan ta kama a yi”, in ji Muhammad Idris.
Ministan ya kuma gargaɗi masu ɓoye kayan abinci da su buɗe shagunansu domin mutane su samu damar saya.
”Ba abu ba ne na alkairi ana cikin wannan matsatsi, kai kuma ka je ka ɓoye abinci don wata manufa taka da daban, don haka gwamnati ke kira ga irin waɗanan ‘yan kasuwa da su fito da waɗanan kayayyaki domin sauƙaƙa wa ‘yan ƙasa”, in ji ministan.
Yana me cewa duk ɗan kasuwar da ya ki bin wanan umarni to gwamnati ta san su ta kuma san matakin da za ta ɗauka a kansu.