Gwamnatin Najeriya ta gargaɗin NLC kan zanga-zangar da ta shirya yi a ƙasar

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar NLC da ta jingine zanga-zangar da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar ranakun 27 da 28 ga wannan wata, kan tsadar rayuwa.

Ministan Shari’a na ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN ne ya bayyana gargaɗin cikin wata wasƙa da ya aike wa lauyan ƙungiyar ƙwadagon, Femi Falana ranar Juma’a.

Ministan ya ce “Gwamnati na ƙoƙarin kammala duka batutuwan da ta cimma da ƙungiyar, kuma abin da ya kamata shi ne NLC ta tuntuɓi gwamnati don tabbatar da aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma, musamman a ɓangarorin da matsaloli suka yi katutu”.

Ya ƙara da cewa zanga-zangar da ƙungiyar ta shirya gudanarwa ta ci karo da umarnin da kotun da ke hukunta laifukan da suka shafi gwamnati da ƙungiyar ƙwadago.

Gwamnati za ta yi maganin masu yi wa kasuwar chanji zagon-ƙasa’

Wuya ta sanya ECOWAS Ta Ɗage Takunkumin Da Ta Sanya Wa Nijar Albarkacin Watan Azumin Ramadana

Ministan ya ce ƙungiyar ta shirya gudanar da zanga-zangar ne saboda zargin gwamnati ta kasa aiwatar da batutuwan da ta cimma da ƙungiyar ƙwadagon ranar 2 ga watan Oktoban bara.

A cikin wasikar ministan ya buƙaci lauyan ƙungiyar ya bai wa ƙungiyar shawarar datakar da zanga-zangar wanda ya ce za ta iya dakatar da ayyukan gwamnati da barazana ga zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *