Gwamnatin Najeriya ta saki babban jami’in kamfanin kuɗin kirifton nan na Binace, wanda ta gurfanar gaban shari’a bisa zargin laifin halatta kuɗin haram, domin ya je a duba lafiyarsa a waje.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon-ƙasa, EFCC, ce ta sanar da sakin Mista Tigran Gambaryan, wanda ke tsare tun watan Afirilu, saboda tsananin rashin lafiya da yake fama da shi a cewarta.
Lauyar hukumar ta EFCC, R. U. Adagba ce ta sanar da kotun tarayyar da ke shari’ar, dakatar da tuhumar, a lokacin zaman kotun, yau Laraba a Abuja, saboda rashin lafiyar jami’in.
Sai dai kuma lauyar ta shaida wa kotun cewa, hukumar ta EFCC, za ta ci gaba da tuhumar da take yi wa kamfanin na Binance Holdings Limited.
Abin da ba a sani ba shi ne yadda za a ci gaba da shari’ar ba tare da mutumin da ke wakiltar kamfanin ba.
Can a baya alƙalin kotun, Justice Emeka Nwite, a karo biyu ya ƙi amsa buƙatar lauyoyin jami’in kamfanin ta bayar da belinsa, bisa dalilan yuwuwar cewa zai iya guduwa daga Najeriya, to amma lauyoyin suka kafe cewa lafiyar Mista Gambaryan ta taɓarɓare a lokacin da yake tsare.
A watan Fabarairu ne hukumomin Najeriya suka kama Mista Gambaryan, wanda ɗan ƙasar Amurka ne tare da shugaban kamfanin a Afirka, Nadeem Anjarwalla, yayin ziyara a Najeriyar kan wasu batutuwa na dokokin aiki da suka shafi kamfanin na Binance.
Sai dai Anjarwalla, ya tsere daga hannun ‘yansanda, ya bar ƙasar, bayan da aka kai shi masallaci ya yi sallah.
Ana tuhumar Gambaryan ne da laifin halarta kuɗaɗen haram da kuma gudanar da kamfanin hada-hadar kuɗaɗe wanda ba shi da lasisi a ƙasar, zargin da ya musanta.
BBCH