Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar ƙwace lasisin gidajen man da ke ɓoye mai

Spread the love

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA) ta yi barazanar ƙwace lasisin gidajen mai da ‘yan kasuwar da aka samu da laifin ɓoye man fetur tare don sayar wa ‘yan bumburutu.

Babban daraktan hukumar, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana haka cikin wani bidiyo da hukumar ta wallafa a shafinta na X, lokacin wata ziyarar bazata da wata tawagar hukumar ta kai wasu gidajen mai a Abuja babban birnin ƙasar.

A ‘yan kwanakin baya-bayan nan ana fuskantar ƙarancin man fetur ɗin a wasu manyan birane da jihohin ƙasar.

A wasu jihohi, musamman da ke yankin arewacin ƙasar, ana fuskantar ƙarancin man, lamarin da ya tilasta wa wasu gidajen mai da dama rufewa, abinda kuma ya haifar da dogayen layuka a gidajen man da ke bayar da man.

Hukumar ta kuma ce sayar wa ‘yan bumburutun man a jarakuna saɓa doka ne tare, sannan kuma hakan na haifar da barazana ga kariyar muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *