Gwamnatin Najeriya ta yi wa ma’aikata kari kan sabon albashi mafi karanci na naira dubu 60.

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon NLC da TUC a wani taron gaggawa da ta gudanar a ranar Litinin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin kasar, George Akume a wani yunkuri na kawo karshen yajin aikin sai abinda hali ya yi da kungiyoyin kwadagon suka fara a jiya Litinin.

Bangarorin biyu sun shafe sa’oi biyar zuwa shidda suna tattaunawa da juna kuma a karshe sun cimma matsaya a kan wasu batutuwa.

Ministan yada labaran kasar Mohammed Idris ya shaida wa BBC cewa gwamnati ta amince ta yi kari a kan naira dubu 60 wanda shi ne sabon albashin mafi karanci na ma’aikata da ta gabatar wa kungiyoyin kwadagon tun farko, wanda suka yi fatali da shi.

Ministan ya yi ikirarin cewa a karkashin yarjejeniyar da suka cimma kungiyoyin kwadagon sun amince su janye yakin aiki:

‘’ Na farko za su janye wannan yajin aiki nasu, na biyu kuma gwamnati ta yi alkawarin za ta sake duba mafi karancin albashi da ake biyan ma’aikata, watau naira dubu 60 domin ayi mu su kari”

”Na uku za a ci gaba da tattaunawa tsakaninmu da ‘yan kwadago, kwamiti da gwamnati ta kafa zai ci gaba da tattaunawa da su na kusan sati daya, kusan kullum za su yi ta ganawa domin a samu sabon tsari na mafi karancin albashin da za a rika biyan ma’aikata” in ji shi.

A dayan bangaren kungiyoyin kwadagon NLC da TUC sun ce za su gudanar taron Majalisar koli a ranar Talata da safe domin su tattauna kan matsayar da suka cimma da jami’an gwamnati.

Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya Komrade Kabiru Ado Minjibir ya shaidawa BBC cewa an baiwa kwamitin da aka dorawa alhakin tsara sabon albashi mafi karanci kwanaki bakwai ya kamala tattaunawa da kungiyoyin kwadago da sauran masu ruwa da tsaki wajan tsayar da mafi karancin albashi:

”A bangarenmu mun yi alkawarin za mu kira taro na Majalisar koli wanda ya hada da wadannan kungiyoyi na NLC da TUC domin a tattauna sannan a fidda matsaya” in ji shi.

Game da maganar wutar lantarki kuwa, kungiyar kwadago ta NLC ta ce majalisar dokokin kasar ta ce ta yi wani kuduri da ya nemi a mayarda farashin kudin lantarki kamar yadda yake a baya

Comrade Minjibir ya ce ‘yan Majalisar dokokin kasar sun yi alkaurin za su ci gaba da bibiya domin su tabbaar cewa wannan umurni nasu, majalisar zartarwa ta yi amfani da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *