Gwamnatin Najeriya za ta fara fito da man Dangote a gobe Lahadi

Spread the love

Kwamitin sayar da ɗanyen man fetur da tatacce na shugaban ƙasa ya ce zai fara ɗauko kashin farko na tataccen mai daga kamfanin Dangote a gobe Lahadi 15 ga watan Satumba.

Ɗaya daga cikin mambobin kwamitin wanda kuma shi ne shugaban hukumar tattara kudaɗen haraji ta ƙasar, (FIRS), Zacch Adedeji, ne ya bayyana haka ranar Juma’a.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, babban birnin ƙasar, shugaban na FIRS ya ce daga ranar 1 ga watan Oktoba, babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL zai fara sayen ganga 385,000 a kowace rana daga matatar man ta Dangote.

Ya kuma ƙara da cewa “Ina kuma farin cikin sanar da ku cewa an kammala duka yarjejeniyar fara ɗauko kashin farko na man fetur da aka tace daga matatar Dangote daga ranar Lahadi 15 ga watan Satumban da muke ciki”, kamar yadda kafofin yaa labaran ƙasar suka ruwaito.

Ya ci gaba da cewa matatar Dangoten za ta riƙa sayar wa Najeriya man fetur da na dizel da zai wadace ta, kuma za a yi cinikin ne da kuɗin ƙasar wato naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *