Gwamnatin Nigeria Ta Kafa Kwamitin Bincike Kan Kisan Matafiya A Edo

Spread the love

Gwamnatin Najeriya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Edo ta kafa kwamitin bincike kan kisan matfiya guda 16 da aka kashe a Uromi a kan hanyarsu ta komawa jihar Kano.

Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Kwamrade Aminu Abdussalam Gwarzo, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Okpebholo ya ce Shugaba Tinubu bai ji daɗin abin da ya faru ba na kisan matafiyan a Uromi, kuma a shirye yake ya bi diddigin lamarin domin kare sake aukuwar lamarin.

“Ina tabbatar muku cewa gwamnatin tarayya da ta Edo sun kafa kwamitin bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru domin magance matsalar baki ɗaya.

“Wannan rahoton da kuka kawo mana zai taimaka wajen sauƙaƙa mana bincike, don haka kada ku damu. Za mu yi abin da ya dace, kuma za mu fitar da sakamakon binciken domin kowa ya gani.”

Mataimakin gwamnan jihar Kano ya yi godiya ga gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *