Gwamnatin Nijar Ta Yanke Hulɗar Soji Da Amurka

Spread the love

Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyyar Nijar karkashin Janar Abdourahamane Tchiani ta sanar da yanke alaƙar soji da Amurka.

Mai magana da yawun gwamnatin, Kanar Abdourhamane Amadou ne ya yi shelar hakan a kafar talabijin mallakin gwamnati a cikin daren jiya na Asabar.

Mai magana da yawun gwamnatin, Kanar Abdourhamane Amadou ne ya yi shelar hakan a kafar talabijin mallakin gwamnati a cikin daren jiya na Asabar.

Sanarwar ta ce Jamhuriyar Nijar ta yanke duk wata alaƙar ayyukan soji da Amurka sakamakon rashin gamsuwa da halaccin yarjejeniyar da aka fake da ita don shigo da dakarun sojin Amurka a kasar ta Nijar a 2012 cikin wani yanayi mai kama da tilastawa ba don rai ya so ba.

Wannan dai na zuwa ne sakamakon gamsuwa da rashin samun wata gudunmawar da ta dace daga Amurka a yunkurin murkushe matsalolin tsaron da ke sanadin rasa rayukan sojoji da al’ummar Nijar.

Da wannan ne kuma gwamnatin ta Nijar ta umurci dakaru 1100 da Amurkar ta girke a sansanoni daban-daban su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba a cewar wannan sanarwa.

Wannan sabon al’amari na zuwa ne a washegarin rangadin da wata tawagar jami’an gwamantin Amurka ta gudanar a Nijar a karkashin jagorancin matemakiyar sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harakokin Afirka, Molly Phee.

A yayin rangadin ne tawagar Molly Phee ta tattauna da Firaiminista Ali Lamine Zeine da wasu mukarraban gwamnatinsa dangane da shirin mayar da Nijar tafarkin dimokuradiya.

Sai dai bayanai sun ce yunkurin ganawar Amurkawan da Janar Abdourahamane Tchiani ya ci tura, lamarin da ke fayyace alamun an yi watsewar baram baram a zaman da ya hada jami’an kasashen biyu.

A wani bangare na sanarwar da Kanar Abdourhamane Amadou ya fitar, hukumomin na Nijar sun nuna rashin gamsuwa da abin da suka kira muguwar halayyar da sakatariya Molly Phee ta nuna a yayin ziyarar ta ranakun Talata, Laraba da Alhamis din da suka gabata .

Hukumomin na Nijar sun yi zargin cewa tawagar ta Amurka ta saba ka’ida ta hanyar zuwa ba tare da wata sanarwa ta gargadi ba.

Hukumomin na Nijar sun yi zargin cewa tawagar ta Amurka ta saba ka’ida ta hanyar zuwa ba tare da wata sanarwa ta gargadi ba.

Hulda a tsakanin Nijar da kasashen Rasha da Iran na daga cikin batutuwan da sanarwar ta hukumomin mulkin sojan Nijar ta tabo, suna masu kare matsayin kasar da suka ce tana da ‘yancin zabin kawayen da suka dace da manufofinta a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *