Gwamnatin jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya ta gargaɗi masu harkokin kasuwanci da mazauna jihar a kan ƙin biyan haraji, inda ta yi barazanar ɗaukar matakin shari’a a kan mutum.
Shugaban hukumar tara kuɗaɗe ta jihar, Mista Olufemi Awakan ne ya yi gargaɗin a wata sanarwa da hukumar ta fitar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce lokaci ya yi da za a biya duk wani haraji da ba a biya ba, kamar yadda doka ta yi tanadi dukkanin wani mazaunin jihar ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na haraji.
Mista Awakan ya ce, biyan haraji ba zaɓi ba ne abu ne da ya zama wajibi kamar yadda yake a sashe na 24 na kundin tsarin mulki Najeriya.