Gwamnatin sojin Nijar ta kafe kan zargin Najeriya da yi mata zagon-ƙasa

Spread the love

Gwamnatin Mulkin sojin Nijar ta tsaya kai da fata, cewa lalle makwabciyarta Najeriya na bayar da mafaka ga masu shirya mata zagon-ƙasa duk kuwa da musanta hakan da Najeriyar ta yi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban gwamnatin mulkin sojan ta Nijar, Janar Abdourrahmane Tchiani ya yi zargin cewa, ƙasashen Benin da Najeriya da Chadi na hada baki da jami’an leken asiri na ƙasar Faransa don kifar da gwamnatinsa, zargin da gwamnatin Najeriya ta ce bai da tushe ko makama.

To amma a hirarsa da BBC, ministan harkokin Nijar Bakari Ya’u Sangare ya ce duk abin da Janar Tchiani ya fada gaskiya ne.

Ministan ya ce suna da tarin hujjoji na maganganun da suka yi kan cewa Najeriya na taimaka wa wajen yi mata zangon-ƙasa, ”muna da hanyoyin samun bayanai,” in ji shi.

A zargin da ya yi a baya shugaban mulkin sojin na Nijar ya ce wasau daga cikin Turawan da suka kora daga Nijar, suna nan cikin Najeriya suna horar da ‘yan ta’dda kuma suna taimaka musu da makamai da dabara iri-iri da za su tayar wa da Nijar hankali.

Najeriya dai ta buƙaci hukumomin na Nijar su ba ta cikakken bayani kan zargin da suke yi cewa akwai wani mutum da ke jagorantar yi wa Nijar din tawaye da ke da sansani a wasu jihohin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *