Gwamnatin sojin Nijar ta rage farashin fetur

Spread the love

Gwamnatin sojin Nijar ta sanar da rage farashin man fetur a fadin ƙasar.

Gwamnatin ta rage farashin fetur ne ƙasa daga CFA 540 zuwa CFA 499, haka ma an rage farashin dan dizel zuwa CFA 618 daga CFA 668.

Gwamnatin ƙasar ta ce matakin zai soma aiki ne daga ranar 23 ga watan Yuli.

Gwamnatin sojin Nijar ta ce manufar rage farashin shi ne rage wa ƴan ƙasa raɗaɗi musamman samun sauki kan farashin sufuri da na kayayyakin masarufi na yau da kullum.

Sai dai masu nazari kan al’amuran yau da kullum na ganin ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki na tabbatar da ganin ‘yan kasuwa a kasar sun sauko da farashin kayayaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *