Gwamnatin jihar Sokoto ta ƙaddamar da sabuwar rundunar ƴan sa kai a jihar.
Gwamnan jihar, Ahmed Aliyu ne ya jagoranci kaddamar da rundunar ta ƴan sa kai, inda ya ce sun kafa rundunar ce domin ta taimaka wajen yaƙi da matsalolin tsaro da ake fama da shi a jihar.
Ya ce an zaɓo ƴan sa kai ɗin ne bisa cancanta, kuma an zaɓo su ne domin taimakawa jami’an tsaro wurin magance matsalar tsaro.
Gwamnan ya yi kira ga jami’an rundunar da su tsaya wajen aiki tukuru, inda ya tabbatar wa al’umma cewa zai cika dukkan alkawuran da ya ɗauka a lokacin yakin neman zaɓe da suka haɗa da samar da tsaro, ilimi, noma da sauransu.
Mun ɗau alwashin ceto mata da kuma ɗalibai da ƴan bindiga suka sace – Gwamnatin Tarayya
Rashin tsaro ya ɗaiɗaita ƴan Najeriya sama da miliyan shida
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda aka ɗaiɗaita dubban mutane da tilasata musu tserewa gidajensu, abin da ya kwatanta hakan da barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da kuma tattalin arzikin ƙasa.
Haka nan, gwamnatin jihar ta samar musu da motoci da kuma babura don samun nasarar ayyukansu.
Yayin kaddamar da rundunar, gwamnonin jihohin arewa maso yamma, sun yi alkawarin aiki tare da kuma samar da tsari guda wajen ganin an magance matsalolin tsaro da yankin ke fama da su.
Da yake magana, gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katina, ya ce haɗin kai daga jihohin zai taimaka ainun wajen shawo kan matsalar tsaro da kuma tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a yankin.
A don haka, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo wa jihohin ɗauki ta hanyar mara wa tsarinsu don kawo karshen rashin tsaro.
Mutanen da suka samu halartar bikin sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Saad Abubakar, gwamnonin jihohin Kano, Bauchi, Benue, Filato da kuma Janar Aliyu Gusau mai ritaya, inda suka yaba wa gwamnan bisa wannan kokari na kafa rundunar tsaro da nufin magance matsalar tsaro.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da ayyukan ƴan bindiga, garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da kuma fashi da makami.
A baya-bayan nan ma, jihohin Katsina da Zamfara suka kaddamar da sabbin rundunonin tsaron, waɗanda suka ce za su ba da gudummawa wajen yaƙi da ayyukan ƴan bindiga da suka addabi jihohin.