Gwamnatin Sri Lanka ta nemi afuwar Musulmai kan tilasta musu ƙona gawa lokacin korona

Spread the love

Gwamnatin Sri Lanka ta nemi afuwar Musulman ƙasar marasa rinjaye game da tilasta musu ƙona gawarwakin ‘yan’uwansu da cutar korona ta kashe a lokacin annobar.

Wata sanarwa ta ce sabuwar dokar da za a kafa za ta ba da ‘yancin zaɓar ƙonawa ko binnewa ga mamatan Musulman da sauran abokan zamansu.

Bisa tanadin addini, Musulmi kan binne gawar ‘yanuwansu ne, amma gwamnatin ta tilasta musu ƙonawa duk da tabbacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar cewa binnewar ba ta da wata matsala.

An dakatar da ƙonawar a watan Fabrairun 2021 bayan kiran da tsohon Firaministan Pakistan Imram Khan ya yi lokacin da yake ziyara a ƙasar ta Sri Lanka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *