Gwamnatin jihar Taraba ta haramta amfani da babura kowane iri a Jalingo, babban birnin jihar
Haka-zalika, gwamatin ta kuma takaita zirga-zirgar Keke Napep daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 8:00 na yamma.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin jihar, ta ce an ɗauki matakin ne sakamakon ƙaruwar ayyukan ta’addanci a kwaryar birnin Jalingo.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin kwamishina ƴan sandan jihar domin ganin haramcin ya yi aiki yadda ake so.
Gwamnatin ta ɗau alwashin kama wa da kuma hukunta waɗanda suka bijire wa haramcin hawa baburan, inda ta ce za a kwace babura da Keke Napep ɗin da suka saɓa dokar sannan a lalata su.