Gwamnatin Najeriya ta ce sauyin yanayi da rashin bin ƙa’idar gine-gine da rashin gyara magunan ruwa ne suka haddasa mummunar ambaliyar da ta auku a garin Mokwa na jihar Neja.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na ƙasar, Farfesa Joseph Utsev ne ya bayyana haka a Abuja babban birnin ƙasar, yayin da yake bayani kan ambaliyar da auka wa garin Mokwa na jihar Neja.
Ministan ya ce ba ɓallewar madatwar ruwa ba ce ta haifar da ambaliyar, yana mai alaƙanta matsalar da ƙaruwar tasirin sauyin yanayi, da kuma ruwan sama da ya wuce kima.
Ya ƙara da ce tawagar ƙwararru daga ma’aikatarsa da kuma sauran hukumomi na garin domin auna irin ɓarnar da lamarin ya haifar.
- Uba Ya Harbe Ɗansa Har Lahira Saboda Zaton Biri Ne
- 2027: Ƙungiyar Shekarau Ta Gindaya Sharaɗi Kafin Shiga Haɗakar Jam’iyyu
Mista Utsev ya buƙaci gwamnatocin jihohi da masu ruwa da tsaki su riƙa la’akari da gargaɗin da hukumomi ke fitarwa tare da aiwatar da matakan kariya.
Garin Mokwa – mai nisan kilomita 350 daga Abuja, babban birnin ƙasar – ya kasance mahaɗar da ta haɗa ƴankasuwa daga arewaci zuwa kudancin ƙasar.
Fiye da mutum 230 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman wasu fiye da 400 bayan mummunar ambaliyar da ta auka wa garin.