Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ware naira biliyan 1.6 domin tallafa wa manoman citta a jihohin uku harda Babban Birnin Tarayya Abuja.
Babban sakataren asusun bunƙasa noman citta, na kasa NADF Mohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a wajen wani taro da aka yi a jahar Kaduna .
ya ce Gwamnatin tarayyara za ta raba wannan tallafi a karkashin Shirin bunƙasa noma na ‘GRATE’.
Ibrahim ya ce akalla manoman citta 15,000 ne cutar ‘Blight’ ya shafa a jihohin Kaduna, Filato, Nasarawa da Abuja a Kuma lokacin da kasar ke bukatar citta domin siyar wa a kasashen waje.
- DSS Da Yan Sanda Sun Kashe Yan Bindiga 18 A Plato
- Kungiyar Arewa Online Journalist Ta Samu Tallafin Buhunan Shinkafa Daga Fatima Aliko Dangote
Sakamakon bincike da hukumar kididdiga ta NBS ta gabatar ya nuna cewa Najeriya ta samu kari a kudaden shiga a dalilin kasuwancin citta zuwa kasashen waje daga naira biliyan 4.6 a 2022 zuwa naira biliyan 10 a shekarar 2023.
Ibrahim ya ce tallafin da gwamnati ta bada za a yi amfani da su, wajen Samar wa manoma ingantattun iri, maganin feshi da takin zamani.
A karshe ya ce suna sa ran tallafin da gwamnati ta bayar zai taimaka wajen bunƙasa noman a kasar.