Ruwan sama babu kakkautawa da ake samu a baya-bayan nan ya sabbaba ambaliya a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja, al’amarin daya sanya Ministan bukatar gwamnatocin jihohin kasar su tsananta kokarin da suke yi na yashe magudanan ruwa.
Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar Muhalli Joseph Terlumum ne ya bayyana wannan damuwa a jawabinsa ga manema labarai a yau Alhamis.
A cewarsa, zuwa Laraba 3 ga watan Yulin da muke ciki, mutane dubu 2 da 102 sun kamu da kwalara sannan ta hallaka 63 tun bayan barkewar annobar.
Ruwan sama babu kakkautawa da ake samu a baya-bayan nan ya sabbaba ambaliya a wasu jihohi da birnin tarayya Abuja, al’amarin daya sanya Ministan bukatar gwamnatocin jihohin kasar su tsananta kokarin da suke yi na yashe magudanan ruwa.
- Babu luwaɗi da maɗigo a yarjejeniyar da muka saka wa hannu – Gwamnatin Najeriya
- Ogun Ta Sa Hausa Cikin Harsunan Faɗakarwa Kan Cutar Kwalara
A cewar ministan, har yanzu babu daya daga cikin madatsun ruwan dake ciki da wajen Najeriya da aka saki.
Ya cigaba da cewa daga watan da muke ciki ake sa ran koguna su fara tumbatsa, kuma jihohin da ake ganin al’amarin zai shafa sun hada da; Akwa Ibom da Anambra da Adamawa da Benue da Bayelsa da Cross River da Delta da Edo da Jigawa da Kogi da Kebbi da Kaduna da Niger da Nassarawa da Ondo da Ogun da Rivers da Taraba da kuma birnin tarayya, Abuja.