Gwamnatin jihar Zamfara ta nesanta kanta daga sulhun da take zargi wasu mutane da take kyautata zaton suna aiki da shirin sulhu da gwamnatin tarayya ta ɓullo da shi don tattaunawa da ‘yan bindigar domin magance matsalar ‘yan bindiga da jihar ke fuskanta.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Comrade Mannir Mu,azu Haidara Kaura, ya fitar ya ce gwamnati Zamfara ta damu matuƙa da yadda wasu mutane da gwamnatin tarayya ta wakilta suke ƙoƙarin yin sulhu da ‘yan bindiga a wasu sassan jihar.
”Gwamnatin Zamfara ta ɗauki wannan yunƙuri a matsayin haramtacce, kuma ya saɓa wa ƙudurin gwamnati da al’ummar jihar Zamfara, don haka gwamnatin Zamfara ba ta goyon bayan matakin”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.
- Tinubu ya taya Mahamat Déby murnar lashe zaɓen Chadi
- Majalisar wakilan Najeriya ta ba da shawarar gina gidajen yari na zamani
Gwamnan jihar Dauda Lawal Dare,ya sha bayyanawa a wurare daban-daban cewa gwamnatinsa ba ta da wani shiri na yin tattaunawar sulhu da ‘yan bindiga.
”Wannan mataki bi-ta-da-ƙullin siyasa ne daga maƙiyan jihar Zamfara, waɗanda ke burin wargaza shirin da gwamnatin jihar ke yi wajen kawar da ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a jihar”, in ji kwamishin yaɗa labaran.
Kwamishin ya ce gwamnatin Zamfara ta yi fatali da wannan mataki da ya ce wasu ke ɗauka na tattaunawa a da ‘yan bindiga a jihar, tare da kira ga jami’an tsaro da ke jihar su sanya idanu tare da hana ayyukan waɗannan mutane a jihar, saboda ya saɓa wa muradin gwamnati da al’ummar jihar.