Gwamnatin Zamfara ta taƙaita zirga-zirgar babur a faɗin jihar

Spread the love

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sanya hannu kan dokar taƙaita zarga-zirgar babura a faɗin ƙasar saboda dalilai na tsaro.

Gwamnan ya amince da matakin ne bayan shawarar majalisar tsaron jihar, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa Sulaiman Bala Idris ya fitar ranar Alhamis ta bayyana.

“Dokar da gwamnan ya sanya wa hannu ta taƙaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 8 na dare zuwa 6 na safe.”

“An umarci jami’an tsaro su hukunta duk wanda aka kama ya saɓa wa dokar,” a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma magance ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *