Gwamnatinmu ba za ta lamunci zubar da jinin ƴan ƙasa ba – Tinubu

Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi allawadai da harin ƙunar baƙin waken da ya kashe aƙalla mutum 18 a garin Gwoza na jihar Borno.

Shugaba Tinubu a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce harin babban abin tashin hankali.

“Masu tayar da rikici su sani cewa za su fuskanci hukunci daidai da su, kuma waɗannan matsoratan da ke kai wa mutane hari, su sani cewa gwamnatinmu ba za ta zura ido ana zubar da jinin jama’a da kuma jefa su cikin tsoro da fargaba ba” inji sanarwar da kakakin shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale, ya fitar.

Shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan mutanen da harin ya ritsa da su, yana mai cewa harin wata alama ce cewa maharan suna fuskantar matsin lamba daga jami’an tsaro dake aikin daƙile ayyukan maharan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *