Gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnatocin jihohin kasar sun cimma matsaya a kan ba wa jihohi wa’adin wata uku kafin su tsame hannnunsu daga lamurran ƙananan hukumomi.
Hakan dai ya biyo bayan damuwar da jihohin suka nuna game da ba wa ƙananan hukumomin ‘yancinsu nan-take saboda tasirin da hakan zai yi kan albashi da kuma wasu abubuwa da suke tarraya a kai.
Wannan dai na nufin ya zama dole ƙananan hukumomin su jira har nan da watan Oktoba kafin su fara samun kuɗaɗensu kai tsaye.
Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya, ya shaida wa BBC cewa, daga cikin abubuwan da aka tattauna yanzu an ba wa jihohin da basu yi zaben ƙananan hukumomi ba damar su yi zaɓe, sannan wannan doka ta fara aiki, domin idan aka ce a fara ba wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu to inda ba a yi zaɓe ba wa za a ba wa ke nan?
Baya ga ba wa jihohi damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi, za su kuma kawo tsare-tsarensu domin akwai abubuwa da akwai haɗaka a ciki a tsakanin jihohi da kuma ƙananan hukumomi kamar ɓangaren ilimi wato hukumar SUBEB, da ɓangaren lafiya a matakin farko to shi ya sa aka bada dama saboda kada a samu matsala.
Gwamna Yahaya, ya ce kuma suna fatan zuwa watan Oktoban jihohin da basu yi zaɓe ba sun yi, sai doka ta fara aiki.
Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin ba wa ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai ne kawai zai iya kawo karshen matsalar Najeriya saboda su ne suka fi kusa da jama’a kuma su suka fi sanin matsalolinsu ta yadda za su magance su.
Sai dai wasu na ganin su ma suna da nasu laifukan wadanda ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, ko da yake sun sha musantawa.