Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Uba Sani, ya ce an gabatar da rahoton kafa ƴansandan jihohi a gaban majalisar tattalin arziki NEC.
A taron na NEC, wanda aka yi a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a ranar Alhamis, ya ƙunshi gwamnoni da mataimakansu da ministoci.
Da yake zantawa da manema labarai bayan taron, gwamna Uba Sani, ya ce gwamnoni da dama sun nuna goyon bayansu kan buƙatar samar da ƴansandan na jihohi saboda yanayin matsalolin tsaro da ake fama da su jihohi.
Sai dai ya ce majalisar ta ɗage tattaunawar zuwa watan Janairun 2025.
“Kusan kowace jiha na da matsalar tsaro da take fuskanta, kuma mafi yawan gwamnonin sun amince cewa ƴansandan jihohi ne za su iya magance matsalar,” in ji shi.