Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin.
Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum.
A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin.
- Yan Sanda Sun Kama Wadanda AKe Zargi Da Satar Wayoyi 23 Da POS A Kano
- Shugabannin sojin Afrika sun kammala taron tsaro a Abuja
Don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon Gwamnatin Tarayya da hukumar NEDC domin gyara manyan gadojin da ruwa ya lalata.
Haka kuma, sun koka kan tsadar kayan aikin gona da suka ce na iya janyo ƙarancin amfanin gona a shekara mai zuwa.
Saboda haka, sun buƙaci a ƙara bai wa manoma tallafi da kuma bunƙasa shirin noman rani.
Bayan haka, gwamnonin sun amince da gudanar da bikin baje kolin kasuwanci na Arewa maso Gabas a Maiduguri a watan Disamban 2025, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar NECCIMA.