Gwamnonin PDP sun buƙaci a kafa ƴansandan jiha

Spread the love

Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya sun yi kira da a kafa rundunonin ƴansanda na jihohi a karkashin wata doka da zata hana yin katsalandan daga duka matakan gwamnati.

Sun jaddada hakan ne a wurin wani taro da suka yi a ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.

Taron ya kuma tattauna yanayin da ƙasar ta tsinci kanta game da wahalhulun da mutane ke fuskanta ta fuskar tattalin arziki da kuma tsaro.

Kotu Ta Ƙi Amincewa Da Buƙatar Mawaƙi Kan Hana BBC Amfani Da Kiɗansa

Kotu ta yanke wa matashin da ta samu da laifin fashin wayar daliba hukunci a Kano

Inda suka buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa wajen ɓullo da wasu shirye-shirye da za su haɗa da duka ɓangarorin gwamnati don samar da mafita mai ɗorewa.

Gwamnonin na PDP sun kuma sha alwashin ci gaba da taka rawar da ta dace domin samar da tsaro ga al’ummansu, abun da a cewarsa ya sa suka jaddada buƙatar kafa ƴansandan jiha.

Taron ya kuma koka kan karyewar darajar kudin ƙasar wato naira, inda suka nemi hukumomin da abun ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalar.

Sai dai jihar Zamfara da ta Filato na daga cikin jihohin da jam’iyyar ta PDP ke mulki, kuma suke kan gaba wajen fuskantar matsalar tsaro da tashe-tashen hankula a tsawon shekaru.

Lamarin da ya yi sanadiyyar asarar dubban rayuka da ta dukiyoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *