Gwmanatin Kano ta rufe babban Ofishin Kamfanin Gine-gine na Ɗantata & Sawoe kan taurin bashin kudin haraji.
Kazalika Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Jihar Kano (KIRS) ta rufe hedikwatar kamfanin jiragen sama na Max Air da kuma kamfanin shinkafa na Northern Rice a Oil Mill, kan rashin biyan haraji.
Daraktan Kula da Basuka na Hukumar, Ibrahim Abdullahi ya ce bayan samun umarnin kotu ne aka rufe kamfanonin.
Ya ce an rufe kamfanin Ɗantata & Sawoe mallakin hamshaƙin attajirin Kano, Alhaji Aminu Ɗantata ne kan bashin harajin albashi na shekara biyu (2021-2022) da ya kai Naira miliyan 241.
- An kama mutum 523 kan satar mutane da ƙwacen waya a Kaduna
- Asibitin kwararru na Best Choice ya rage kaso 30 cikin 100 a ayyukan kula da hakora
Kamfanin Max Air, mallakin Alhaji Sagiru Barau Mangal babban attajirin Jihar Kastina — kuma surukin uban gidan gwamnan Kano mai ci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso — kuma an rufe shi ne kan taurin bashin harajin shekara biyar (2017 zuwa 2022).
Jami’in ya ce an rufe kamfanonin ne bayan an yi ta rubuta musu takardu su biya kuɗaɗen ba tare da nasara ba.
Ya ce dukkansu za su ci gaba kasancewa a rufe har sai sun biya kuɗaɗen, yana mai cewa yin hakan ya zama dole domin tabbatar da ba sa ƙwarar jihar a kuɗaɗen harajinta domin samar da ayyukan cigaban al’ummar