Hafsat Chuchu : Babbar Kotun Kano Ta Yanke Wa Malamin Da Ya Yi Wa Nafiu Hafiz Wankan Gawa Hukunci.

Spread the love
Hafsat, mijinta Dayyabu Abdullahi , Malam Adamu.

 

Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 3 karkashin jagorancin Mai Shari’a Faruk Lawan, ta yanke wa Mallam Adamu, hukuncin daurin watanni shida a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya, da kuma biyan tarar naira dubu 50,000, sannan kuma zai shafe watanni shida yana koyar da daurarru alkur’ani mai girma, bayan samun sa da laifin yi wa Nafi’u Hafiz wankan gawa.

Ana zargin Hafsat Surajo, da hallaka wani hadimin gidanta mai suna Nafi’u Hafiz, tun a ranar 21 ga watan disambar 2023 a jahar Kano.

An karanto wa Hafsat Surajo ( Chuchu) da kuma mijin ta Dayyabu Abdullahi, kunshin tuhumar da ake yi mu su, amma mijin nata ya musanta zargin, ya yin da Hafsat ta yi gum da bakinta.

Hakan ya sanya lauyoyin dake kare ta , suka roki kotun a tura ta wajen likitoci don a duba lafiyar kwakwalwarta.
Sai dai lauyan gwamnatin jahar Kano, Barista Halima Yahuza Ahmad , ta yi suka kan rokon.

Alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Yuni 2024.

jaridar idongari,ng, ta ce tun a ranar 21 ga watan Disamba, 2023, ake zargin Hafsa Suraj, da yin amfani da wuka inda ta caccaka wa marigayin a kirjinsa da wasu sassan jikinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

Ana tuhumar Hafsat Suraj da laifin kisa, laifin da ya saba da sashe na 221 na kundin penel code.

Tun bayan cafke wadanda ake zargi da hannu cikin lamarin, Kwamishinan yan sandan CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce bayan binciken da suka gudanar, sun gano mijin matar mai suna Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma wani Mallam Adam, nada hannu a yunkurin binne marigayin ba tare da sanin yan uwansa ba.

Mijin matar ya bayyana cewa, ya fara kiran yan uwan marigayin a waya da suke can jahar Bauchi inda ya fada musu cewar ya rasu amma bai sanar da dasu musabbabin rasuwarsa ba.

Ya kara da cewa marigayin shi ne yake kular masa da wasu kayayyakin kasuwancin sa, sai dai mijin matar da ake zargi ya ce, matar tasa tasha furta masa kalaman kisan ko kuma ta yi yunkurin kashe kanta.

Idan ba a manta ba, Mallam Adamu da ake zargi da yi wa Nafi’u wankan Gawa , ya shaida wa Idongari.ng cewa mijin matar ne, ya kira shi a waya har ya bayyana masa cewar, an yiwa marigayin aikin Basir amma ya mutu.

Ya kara da cewa bayan yaje gidan ne sai yaga jikinsa da alamun yankan wuka, bayan ya tambayi mijin matar , sai ya shaida masa cewa matarsa ce ta caccaka masa wuka.

Mallam Adamu ya ce, ganin abunda ya faru ne ya ce mu su ,ba zai iya ba,amma sai matar ta ce matukar ba iyi wankan ba zata kashe kanta, shi kuma ganin ta furta kalaman kisa ne yasa shi yin wankan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *