Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta buƙaci maniyyatan bana da su yi gaggawar biyan N1,918,032.91 ƙari a kan kuɗin kujerar Hajjin bana.
Hukumar ta bai wa maniyyatan da ke son sauke farali a bana da su gaggauta cika kuɗin daga yanzu zuwa ƙarfe 11:59 na daren 28 ga Maris, 2024.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar alhazan, Farima Sanda Usara ta fitar a Yammacin wannan Lahadin.
Hajiya Usara ta ce hukumar za ta rufe karɓar cikon kuɗin ne a ranar 29 ga watan Maris, kuma daga wannan lokaci babu wani maniyyaci da za su saurara matuƙar bai biya kuɗin kafin lokacin ba.
- Mutum 3 Sun Shiga Hannu Kan Yunkurin Sace Wani A Bauchi
- Ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun janye yajin aiki
A yanzu dai bayan wannan ƙarin, duk wani maniyyaci zai biya kusan Naira miliyan bakwai matuƙar yana son sauke farali a bana.
Ana iya tuna cewa, tun a watan Fabarairun da ya gabata ne hukumar alhazan ta ƙayyade kusan naira miliyan biyar a matsayin kuɗin kuejrar hajjin bana.
Sai dai tun bayan lokacin, hukumar ta soma tababar ƙara wa maniyyatan kuɗi a dalilin tsadar Dala da ke neman hana yi wa maniyyatan dawainiyar da aka saba yi musu ta masauki, abinci da makamantansu.
A wancan lokacin dai, NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudancin Najeriya su biya naira miliyan 4,899,000, yayin da maniyyatan Arewa za su biya naira miliyan 4,699,000.
Sai kuma maniyyatan jihohin Yobe da Maiduguri da aka ƙayyade kuɗin kujerarsu a kan naira miliyan 4,679,000.