Halilu Buzu: Ɗan Nijar ɗin da sojojin Najeriya ke nema ruwa-a-jallo

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta buƙaci hukumomin jamhuriyar Nijar su kama mata wani mutum da suka bayyana da shugaban wata babbar ƙungiyar garkuwa da mutane.

An kuma zargin Halilu Buzu -wanda ɗan ƙasar Nijar ne – da laifin safarar makamai da satar shanu da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a jihar Zamfara da ke Najeriya, inda ake yawan samun laifukan garkuwa da mutane.

Hukumomin Najeriya sun jima suna bayar da rahoton kama mutumin ya yi fice a fannin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun Manjo Janar Edward Buba mai magana da rundunar tsaro ta Najeriya, ta ce Halilu Buzu ya yi daba ne a dajin Subbubu da ke jihar Zamfara.

Ta kuma ƙara da cewa yana da daba da wurin haƙar zinare a ƙaramar hukumar Anka ta jihar ta Zamfara.

Hukumomin na Najeriya na zargin Halilu Buzu ne da kasancewa ƙasurgumin mai satar shanu da haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba.

Sanarwar hukumar tsaron ta Najeriya ta ce yaran Halilu, a lokacin wani hari da suka kai a makon da ya gabata sun kashe mutum 19 a ƙauyen Farar ƙasa.

Ana kuma zargin Buzu da laifin kasancewa ƙasurgumin mai safarar makamai daga ƙasashe masu maƙwaftaka zuwa cikin Najeriya.

Me ya sa sojojin Najeriya suka kasa kama Buzu?

A cikin sanarwar da shalkwatar tsaron ta Najeriya ta fitar ta ce ta gaza kama Halilu Buzu ne saboda yakan ƙetare zuwa Jamhuriyar Nijar da zaran sojoji suka matsa masa.

“A duk lokacin da sojoji suka kusa cim masa sai ya tsallaka zuwa cikin Jamhuriyar Nijar,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Shi ya sa a yanzu Najeriyar ke bin matakan da ta ga sun kamata wajen ganin ta kama shi.

“Muna kira ga hukumomin Jamhuriyar Nijar su kama shi tare da tuhumar sa kan irin munanan abubuwa da ya aikata.

Zamfara na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya waɗanda ke cikin ƙangin ayyukan ƴan bindiga masu garkuwa da mutane da satar dukiya da kuma kisa.

Jihar na daga cikin waɗanda aka fi kashe mutane shekarun baya-bayan nan sanadiyyar ayyukan ƴan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

A wata hira da BBC, ɗan majalisa mai wakiltar Zurmi da Shinkafi a majalisar wakilan Najeriya, Bello Hassan Shinkafi ya ce yanzu haka akwai mutane aƙalla 500 da ƴan bindigar suka yi garkuwa da su daga ƙauyukan yankin.

Tarihin ayyukan Halilu Buzu

Wani ɗan jarida mai nazari kan tsaro a arewa maso yammacin Najeriya, Mannir Fura-Girke ya bayyana wa BBC cewa Halilu Buzu na daga cikin ƴan bindiga mafiya ƙarfi a yankin.

“Kusan a yankin arewa maso yamma babu wanda yake da ƙarfin shi ta fannin dukiya da kuma makamai.” In ji Fura-Girke.

Kamar yadda sanarwar sojojin ta bayyana, Halilu Buzu a cewar Mannir ya shahara ne a kan abu uku: Satar shanu da garkuwa da mutane da safarar makamai sai kuma haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

A farko Halilu Buzu ya fara ayyukansa na laifi ne da satar shanu, daga nan sai ya koma garkuwa da mutane da kuma safarar makamai daga ƙasashe masu maƙwaftaka da Najeriya, kamar Jamhuriyar Nijar har ma da Libya yana sayar wa ƴan bindiga a Najeriya.

Sannan kuma an bayyana cewa a yanzu ya fi mayar da hankali ne kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *