Hanya ɗaya tilo da ta rage wa Arsenal cin kofin Premier

Spread the love

Da maraicen yau ne za a ƙarƙare wasu daga cikin gasannin nahiyar Turai da wasu sassan duniya, ciki har da Premier League ta ƙasar Ingila.

A wasu gasarnin ƙasashen tuni aka samu waɗanda suka lashe su, kamar Bundesliga da La Liga da Serie A.

Amma a gasar Premier Ingila har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin kuwa wasan na yau shi ne zai zama raba-gardama tsakanin Pep Guardiola da Arteta.

A yanzu haka Manchester City ce ke jagorantar teburin da maki 88 tazarar maki biyu tsakaninta da Arsenal mai 86.

Arsenal na fatan ɗaukar kofin karo na farkon cikin shekara 20, yayin da Manchester City ke fatan kafa tarihin lashe kofin karo huɗu a jere.

Ko wace hanya Arsenal za ta bi domin ɗaukar kofin?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *