Har Yanzu Ba A Ba Mu Umarnin Kamo Ado Gwanja Ba — SP Abdullahi H. Kiyawa

Spread the love

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano, ta bayyana cewa har kawo yanzu ba ta samu wani umarni na kamo mawaƙi Ado Gwanja ba.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A cewar saƙon da Kiyawa ya wallafa, “zuwa yanzu ba mu samu umarnin kotu na kamo Ado Gwanja ba.

“Da zarar an ba mu [umarni] za mu aiwatar,” in ji Kiyawa.

Ana iya tuna cewa, a ranar Litinin da ta gabata ce wata Babbar Kotu a Jihar Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta ba da umarnin kamo mawaƙi Ado Gwanja.

Gwamnatin Kano Zata Dafawa Aiyukan Hukumar Hisbah Don Yaki Da Badala A Tsakanin Al’umma.

Yan sanda sun kama mai sace jama’a da ake nema ruwa a jallo a Abuja

Bayanai sun ce kotun ta kuma haramta wa mawaƙin yin waƙa har zuwa lokacin da ’yan sanda za su kammala bincike a kansa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ta maka mawaƙin a kotu kan amfani da kalaman da ba su dace ba a waƙoƙinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *