Harin bam ya kashe mutum ɗaya a jihar Borno

Spread the love

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, Nema, ta bayar da rahoton tashin wani bam a kan babbar hanyar Damboa na jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Hukumar ta ce dakarunta na kai agajin gaggawa sun gudanar da aikin haɗin gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki domin kwashe waɗanda fashewar ta rutsa da su zuwa asibitin ƙwararru na jihar.

An samu rahoton cewa mutum ɗaya ya rasu a hanyar zuwa asibitin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da wani ayarin motocin haya da suka taso daga Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Damboa suka ci karo da bam ɗin da ake zargin ƴan bindiga ne suka dasa

facebook  idongari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *