Harin Jiragen Sojojin Nigeria Ya Kashe Mutane 10 A Sokoto

Spread the love

Wasu hare-haren da sojojin Najeriya na sama da na ƙasa suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto sun yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 10 da raunata wasu da dama.

Lamarin ya faru ne da safiyar Laraba, yayin da jami’an sojin suka kai hari kan ƙauyukan, kamar yadda shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar wa BBC.

A tattaunawarsa da BBC, Abubakar Muhammad ya ce “Tun da safe aka kira ni aka shaida min cewa an ji saukar bama-bamai, inda na bincika na tabbatar da faruwar hakan.”

Shugaban ƙaramar hukumar, wanda ya bayyana cewa shi da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na daga cikin waɗanda suka yi jana’izar mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin harin, ya ce “jirgin yaƙi guda biyu ne suka saki bama-bamai” a kan ƙauyukan.

“Wani wuri ne da ake kira Gidan Bisa da kuma Runtuwa waɗanda ke a mazaɓata.”

“Hare-hare ne babu ƙaƙautawa,” waɗanda Abubakar ya bayyana cewa sojojin ba su tsaya da kaiwa ba har sai da gwamnatin jihar ta sanya baki.

Ya ƙara da cewa “Sojojin sama ne da na ƙasa suka kai harin, sojojin sama sun shiga yankin da manyan tankokin yaƙi.”

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce baya ga mutum 10 da suka mutu, akwai kuma mutum shida da suka samu raunuka.

Ƙauyukan na kusa da jejin Surame da ake ganin maɓuyar mayaƙan ƙungiyar Lakurawa da ta ɓulla a ƙasar a baya-bayan nan.

A lokuta da dama sojojin Najeriya kan yi kuskuren kai hare-hare kan fararen hula, lamarin da a wasu lokutan ke haddasa mummunan asarar rayuka.

Ko a watan Disamban 2023 ma, wani jirgin sojin ƙasar maras matuƙi ya kai hari kan masu Mauludi a garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, lamarin da ya haifar da asarar gomman rayuka, da jikkata wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *