Wani mummunan Hatsarin Mota ya Yi sanadiyar rasa rayukan mutane 14 a jahar Jigawa.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Jigawa, DSP Shisu Lawan Adamu, ne ya tabbatar da hakan a Wani takaitaccen sako da ya aike da manema labarai, a ranar Litinin.
Sai dai rahotanni na cewa direban motar ya na nan a raye.
Kawo yanzu Rundunar ba ta bayyana musabbabin faruwar lamarin ba.