Hukumar ƙididdiga a Najeriya NBS ta ce hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris.
A shafinta na X, hukumar ta ce hauhawar ta ƙaru ne daga kashi 31.7 cikin 100 na watan Fabarairu.
A cewar hukumar, wannan ya nuna hauhawar farashi ta ƙaru da da kashi 11.16 cikin 100 a watan Maris ɗin 2024 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Maris na 2023 da ya kasance kashi 22.04 cikin 100.
Kazalika ƙididdigar da NBS ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashi a Maris ɗin 2024 ta kai kashi 3.02 cikin 100 saɓanin kashi 3.12 cikin 100 da aka gani a watan Fabarairu.
- DSS ta kama makusanciyar El-Rufai kan sukar gwamna Uba Sani
- NLC ta nemi sabon albashi mafi ƙaranci ga ma’aikta na N615,000
Hakan na nufin a watan Maris, ƙaruwar farashin kayayyaki ba ta kai wadda aka gani ba a watan Fabarairu.
Hauhawar farashi a watan Maris ta faru ne a lokacin da matakan da babban bankin Najeriya ke ɗauka na ɗaga darajar naira kan kuɗaɗen waje suka fara tasiri.
A makonnin baya-bayan nan darajar naira ta ƙaru a kan dala da fiye da kashi 40 cikin 100 daga kusan naira1,900 kan kowace dala zuwa kusan naira1,100 duk dala ɗaya.
Najeriya ta fuskanci hauhawar farashin da ba a taba gani ba a baya-bayan nan sakamakon faɗuwar darajar naira da kuma janye tallafin mai da gwamnati ta yi.
Sau biyu babban bankin ƙasar na ƙara kuɗin ruwa a bana a ƙoƙarin daidaita farashin kaya.