Yan Sandan Kano Sun Sake Cafke Karin Matasan Yan Daba 61 Dauke Da Makamai Da Miyagun Kwayoyi.

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta sake samun nasarar Kama wasu matasa 61, da ake zargi da yunkurin tare hanya don aikata laifukan Daba da yin kwace ga wadanda suka halacci bikin Hawan Daushe a masarautun jahar guda biyar da suka hadar da, Masarautar Kano, Bichi, Rano, Karaye da Gaya.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da manema labarai da yammacin ranar Juma’a.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce gamayyar hukumomin tsaron jahar ne suka cafke Matasan yan daban dauke da makamai daban-daban da kuma Miyagun kwayoyi.

Hukumomin Tsaron da suka Yi farautar wadanda ake zargin sun hada da , Yan sanda, Sojoji, DSS, CIvil Defence, NDLEA da Kwastam.

Sauran sune hukumar gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, hukumar kula da shige da fice, FRSC, Hisbah da kuma Karota.

Jaridar idongari. ng, ta ruwaito cewa, yanzu haka wadanda ake zargi suna ci gaba da bayar da hadin kai ga jami’an yan sanda wajen gudanar da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su a gaban kotu.

Idan ba a manta jaridar idongari. ng, ta ruwaito mu Ku cewar, Rundunar yan sandan ,ta cafke wasu yan Dabar siyasar 54, dauke da muggan makamai da kwayoyi a ranar Idin Sallah tare kuma da gano yukurin da wasu ke yi na hana gudanar da bikin hawan Daushe a fadar sarkin Kano a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilun 2024.

Sanarwar ta ce rundunar yan sandan ta gano makircin da wasu marasa kishin Kano da zaman lafiyarta ke shiryawa ne ya basu damar kara yawan jami’an tsaro don kare rayukan al’umma da dukiyoyin tare tabbatar da an kammala bukukuwan sallar lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *