Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta fara bai wa ‘yan Najeriya biza’

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta ɗage haramcin bai wa ‘yan Najeriya biza nan ba da jimawa ba.

Ministan harkokin sufirin jiragen sama na Najeriya, Festus Keyamo wanda ya shaida haka a watan tattaunawa da wani mataimaki na musamman ga shugaba Bola Tinubu, Otega Ogra, da ke kan manhajar Youtube kamar yadda jaridar Daily Trust ta ce.

Keyamo ya ce shugaba Tinubu ya cimma matsaya da shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al nahya a lokacin da ya kai ziyara ƙasar a watan Satumbar 2023.

Sai dai kuma mista Keyamo ɗin ya ce duk da cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun gindaya ƙarin wasu sharuɗɗa kafin ɗage hanin bayar da bizar, amma tuni Najeriya ta kammala dukkannin wasu stare-tsare da ke nuni da yiwuwar ayyana dage hannin daga UAE nan ba da jimawa ba.

Ɗage wannan hani dai ana tsammanin zai janyo sauƙin tafiye-tafiyen ƴan Najeriya zuwa ƙasar ta UAE, ta hanyar huɗar kasuwanci da ci gaba tsakanin ƙasashen biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *