Hedikwatar tsaro ta yi watsi da jita-jitar juyin mulki a Najeriya

Spread the love

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta yi fatali da zargin da wata kafar yaɗa labarai ta intanet ke yaɗawa kan iƙirarin cewa an sanya masu tsaron fadar shugaban ƙasa a shirin ko ta kwana bayan zarge-zargen da ake yi kan fargabar kifar da gwamnati.

Wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Brigadiya Janar Tukur Gusau ya ce an ankarar da su game da wani rahoto da aka wallafa a intanet a ranar 25 ga watan Fabarairun 2024 da ke iƙirarin cewa masu tsaron fadar shugaban ƙasa na cikin shirin ko ta kwana sakamakon wasu alamu da ke janyo fargabar yin juyin mulki a Najeriya.

“Rahoton ya kuma ce zargin ya janyo yin taron gaggawa tsakanin shugaba Bola Tinubu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa.

Hedikwatar tsaron ta ƙaryata labarin inda ta ce an tsara masu tsaron fadar shugaban ƙasa su kare fadar da kuma babban birnin tarayya da kewayenta.

A cewar hedikwatar tsaron, a kullum jami’an tsaron da ke fadar shugaban ƙasa na cikin shirin ko ta kwana domin sauke nauyin da aka rataya a wuyansu.

NLC ta zargi gwamnatin Najeriya da shirya kai mata hari

Jama’ar Garin Sheka Ku zauna lafiya, kar Abun da ya faru ya zama tashin hankali: Dagacin Sheka.

Hedikwatar ta kuma yi waiwaye kan yadda babban haftsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya sha nanata ƙudurin jami’an sojin Najeriya na kare martabar dimokradiyyar ƙasar.

A don haka hedikwatar tsaron ta yi kakkausar suka kan zargin inda ta buƙaci jama’a su yi watsi da shi.

Hedikwatar ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta ɗaukan mataki kan jaridar da ta wallafa labarin saboda mataki ne na rashin nuna kishin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *