Hedikwatar tsaron Najeriya ta gargadi kungiyar HURIWA kan rikicin Filato

Spread the love

Hedikwatar tsaro ta Najeriya, ta ja hankalin kungiyoyi masu kokarin ta’azzara al’amura a daidai lokacin da sojojin suke iya bakin kokarinsu dangane da samar da zaman lafiya yankin da ke fama da rikici a jihar Filato.

Wannan dai na dauke a cikin wata sanarwa da hedikwatar ta fitar mai sa hannun darektan yada labaranta, Burgediya Janar Tukur Gusau ranar Litinin din nan a Abuja.

Birgediya General Gusau dai ya maryar da martani ne ga kungiyar HURIWA ta marubuta masu rajin kare hakkin bil’adama wadda ta soki kwamitin da aka kafa domin samo bakin zaren rikicin da ya dabaibaye yankin na jihar Filato.

Yan sandan Kano sun cafke kasurgumin mai garkuwa da mutane, satar shanu, da suka addabi Birnin Gwari,Katsina, Zamfara.

Ya ce kwamitin wanda babban hafsan sojojin kasar ya kafa da kansa na karkashin jagorancin tsohon babban soja mai tarin kwarewa.

Kugiyar ta HURIWA dai a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi ta hannun shugabanta na kasa, Emmanuel Onwuboik, ta soki babban hafsan sojin kasar inda ta ce ba da gaske yake yi ba wajen warware rikicin na jihar Filato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *