Herbert Wigwe ya taimake ni bayan an sauke ni daga sarkin Kano

Spread the love

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmowa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’an bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalinsa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.

“Na yi tunanin zan riga mista Herbert rasuwa. duka mun san irin kirkinsa, da biyayyarsa,” in ji Muhammadu Sanusi ll, lokacin da yake jawabi muryarsa cike da alhinin.

Ya ce tsohon jami’an bankin na Acces ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce a lokacin har jirgin sama mista Herbert ya tanadar masa don ɗaukarsa daga Kano zuwa Legas.

“A lokacin da na samu matsala a Kano, wata shida kafin a sauke ni, na kira shi na faɗa masa halin da ake ciki, sannan na ce masa, ‘Herbert na san irin ƙoƙarin da kake yi wajen magance wannan matsala, amma na san saukeni za a yi”.

“Sai ya ce mini ”mai martaba, kada ka damu. duk abin da ya faru kar ka damu muna tare da kai. A ranar da na ji sanarwa a radiyo cewa an saukeni, sai na kira shi na ce masa ina son zuwa Legas”.

An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi don cire dala miliyan 6.2 a CBN’

Yansanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa da mutane a Najeriya

“An yi sanarwar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, zuwa da rana Herbert ya tanadar mini da jirgi a filin jirgin sama na Kano, sai dai a lokacin an tsara cewa za a kaini zaman gudun hijira nashekaru masu yawa, daga nan sai na saka iyalina cikin jirgin tare da tura su Legas, ban yi waya da shi ba, amma ya tarbe su tare da sauke su a otal, kafin daga baya ya sama musu muhalli, inda suka kwashe watanni suna zaune kafin na komo Legas don ci gaba da zama tare da iyalaina”.

Muhammdu Sanusi ll ya kuma ce mista Herbert ya yi masa alkawarin ɗaukar nauyin tafiye-tafiyensa bayan komawa Legas da zama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *