Ƙungiyar Hezbollah a Lebanon ta ce ta kai harin roka zuwa arewacin Isra’ila ranar Asabar.
Hezbolla ta ce harin nata ramuwar gayya ce ga wani hari ta sama da Isra’ila ta kai kudancin Lebanon.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kakkaɓo wasu makamai da ta yi ƙiyasin sun kai 30.
Rahotonni sun ce wasu makaman sun faɗi ne a wurin da babu jama’a a yankin Upper Galilee da ke arewacin ƙasar, inda suka tayar da gobara.
Musayar wuta a kan iyakokin Isra’ila da Lebanon tsakanin Hezbollah – da ke samun goyon bayan Iran – da sojojin Isra’ila na ci gaba da ƙaruwa a makonnin baya-bayan nan, lamarin da ke haifar da fargaɓar ɓarkewar sabon yaƙi a yankin Gabas ta Tsakiya.