Hisbah Ta Gayyaci Matashiyar Da Ta Yada Bidiyon Zargin Aikata Badala A Wani Gida Dake Kano.

Spread the love

Kano

Hukumar Hisbah Ta jahar Kano, ta gayyaci wata Matashiya Mai suna Nana Haruna wadda akafi sani da (Nancy), sakamakom Sakin wani faifen Bidiyo a shafukan sada zumuntar Zamani, har ta zargi wasu mutane da aikata Badala, a wani Gida dake unguwar Kofar Kabuga a birnin Kano.

Sakin da faifen Bidiyon ya janyo cece-kuce a wajen ma’abota shafukan sada zumuntar, Inda kiraye-kiraye suka Yi wa hukumar Hisbar yawa kan batun Sakin Bidiyon da matashiyar ta Yi.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa hukumar ta gayyaci Nana Haruna, a ranar Litinin, domin ta Yi karin bayani kan Bidiyon da ya tayar da kura.

Babban kwamandan hukumar Hisbah Asheik Dr. Aminu Ibrahim Daurawa, bayar umarnin gayyatar matashiyar karkashin jagorancin Mukaddashin babban kwamandan hukumar Dr. Mujahidin Aminuddin Abubakar.

Dr. Mujahidin Abubakar, ya ce budurwa ta zargi wasu mutane da aikata ba daidai ba, Wanda lamari ya yadu har ya yamutsa hazo.

Ana ta bangaren Nana Haruna, ta bayyana cewa faifen Bidiyon da ta saki, tabbas Hisbah ta kira ta kuma sun gana da kwamandan hukumar Hisbah Asheik Dr Aminu Ibrahim Daurawa, Amma duk Mai Neman ta ya Yi hakuri ya zo Hisbah don Jin karin bayani.

Download Audion da yake kasa domin sauraren tattaunawar su da Hisbah

AUD-20240826-WA0035

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *