Hisbah Ta Kamo Maza Da Mata Da Ake Zargi Da Siyar Da Giya Da Kuma Yawon Banza A Kano

Spread the love
Hisbah Kano

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta Kama wasu maza da Mata Su 20 wadanda ake zargi da siyar da Giya da kuma yawon banza a sassan jahar.

Babban Daraktan hukumar Hisbah na jahar Kano, Malam Abba Sa’idu Sufi Danbatta, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Ranar Laraba.

Hukumar Hisbar ta ce ta yi nasarar kamo wadanda ake zargin ne Bayan samun rahotannin sirrin kan yadda ake siyar da Giya a garin Dakatsalle Kano.

Abba Sufi , ya ce Kano jaha ce wadda ta ke gabatar da dokoki bisa shari’ar addinin Musulinci , kuma daman Jami’an Su a koda yaushe a shirye suke don fita aikin dakile batagari.

An dai kamo Giyar a garin Dakatsalle, Bayan samun Bayan sirrin siyar da Barasar a yankin duk da haramcin Hana siyar da ita a fadin jahar.

Ya Kara da cewa Jami’an Su sun Kai sumamen a Ranar Talata da daddare , Zuwa wajen da ake zargin Ana siyar da siyar da Barasar, har aka yi nasarar kwaso giyar da kuma wasu Mata da suke yawon banza.

Haka zalika ya ce an Kai wani sumamen a kwanar Bagauda, inda ake zargin Ana sabawa Allah, inda aka kamo Mata da Maza kuma za a Fara tantance Su domin Kai Su gaban kotu, kamar yadda Doka ta tanada.

Sai dai Babban Daraktan hisbar ya koka, kasancewar sau biyar siyar Kama giya a wajen, kuma Alkalin kotu ya yi mu Su gargadi kan Su daina mu’amullar da suke yi.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa wasu daga cikin wadanda aka Kama din sun fito daga jahohin Katsina, Plato, Kano da dai sauransu.

” Yanzu ya rage na Alkali ya dauki hukuncin da ya da ce, mu abunda mu ke yi shi ne mu kamo, sannan mu Kai wa Alkali shi kuma ya yanke hukunci na yawan Saba wa dokoki da kundin tsarin mulki na jahar Kano ” Abba Sa’id Sufi”.

A karshe ya yi Kira ga al’umma da Su dinga sanar da hukumar dukkan wani waje da ake yada Fasadi don daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *